Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Shugabar Taiwan Ta Kawo Ziyara Kasar Amurka


Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen
Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen

Cikin shekaru 15 da suka gabata wannan ne karon farko da wata shugabar kasar Taiwan ta ziyarci kasar Amurka lamarin da tuni China ta yi Allah wadai dashi tana cewa ba za ta amince da duk wani yunkurin samar ma kasar Taiwan 'yancin kai ba

A wannan makon ne shugabar Taiwan take ziyarar birnin Los Angeles, wanda zai kasance karon farko a cikin shekaru 15, da wata shugabar Taiwan za ta yi magana a bainar jama'a a Amurka, a wata alamar kara karfin dangantaka tsakanin hukumomin Amurka a Washington, da takwarorin su dake birnin Taipei.

Shugaba Tsai Ing-Wen, ta gana da wakilan majalisar dokokin Amurka, da 'yan Taiwan dake Amurka a ranar Litinin da jiya Talata, lamari da ya sa China a hukumance ta fadawa Amurka rashin jin dadinta. China tana daukar Taiwan a zaman wani lardin kasar da ya fandare.

Wakili a majalisar wakilan Amurka Brad Sherman, wanda jigo ne a kwamitin kula da harkokin ketare shiyyar asiya da yankin Pacific a majalisar, ya gayawa Muryar Amurka cewa, yana fatar wani lokaci nan gaba shugaba Tsai za ta kawo ziyara nan birnin Washington.

Jiya Talata, ofishin China mai kula da Taiwan, ya sake nanata rashin amincewar sa ga duk wani yunkuri na goyon bayan Taiwan ta sami 'yancin kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG