Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantaka Tsakanin Amurka Da Turkiya Na Kara Muni


Karamin jakadan Amurka a Turkiya Jeffrey Hovenier yayinda ya ziyarci Pastor Andrew Brunson inda ake tsare dashi a Turkiya.
Karamin jakadan Amurka a Turkiya Jeffrey Hovenier yayinda ya ziyarci Pastor Andrew Brunson inda ake tsare dashi a Turkiya.

Bisa duka alamu rikicin dake tsakanin Amurka da Turkiya bai nuna alamar karewa ba, maimakon hakan ya na dada fadada ne

Babu alamar tabarbarewar dangantakar Amurka da Turkiyya ta zo karshe yayin da lamarin ke ci gaba da munana.

Turkiyya ta kasance mamba a kungiyar tsaro ta NATO,kawar Amurka, wacce ke dauke da wani muhimmin sansanin sojin saman Amurka da ke Incirlik, wanda ya kasance mashigi ga tekun Bahr Aswad da dakarun sojin ruwan Amurka ke yawan amfani da shi.

Shugaban Amurka Donald Trump na ta fushi da kasar ta Turkiyya, saboda wani Pastor Brunson dan Amurke da take tsare da shi hade da wasu Amurkawa da ma’aikatan diplomasiyya, a cewar Sakatariyar yada labarai a Fadar White House, Sarah Huckabee Sanders.

Wata majiya ta kara da cewa akwai karin takunkumi da ake duba yiwuwar saka su akan Turkiyyan.

Ita Turkiyya na zargin paston mai suna Andrew Brunson da laifin yin leken asiri, ta kuma yi mai daurin talala inda ake jiran a kai shi gaban kuliya.

Shugaban rikon kwarya na ofishin jakadancin Amurka da ke Ankara, babban birnin Turkiyyar, Jeffery Hovenier, ya ziyarci Paston a jiya Talata, ya kuma nemi da a sasanta lamarin cikin lumana da adalci ba tare da bata lokaci ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG