An ga jami'ai suna fitar da gawarwaki daga cikin tarkacen motar bas din, wadda ta tashi daga birnin Guadalajara da ke yammacin jihar Jalisco zuwa Los Mochis a Sinaloa.
"An kidaya gawarwakin mutane goma sha tara da suka mutu," in ji Sara Quinonez, atoni janar ta jihar Sinaloa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, inda ta kara da cewa za'a dauki lokaci kafin a iya gane wadanda lamarin ya shafa.
Babbar motar da motar bas din dauke da mutane kusan 50 sun yi taho-mu-gama ne kafin ta su kama da wuta, Roy Navarrete, a cewar daraktan kare fararen hula a Sinaloa, a wani taron manema labarai.
Hukumomin kasar na gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin da ya afku kafin wayewar gari a wata babbar hanya a karamar hukumar Elota.
Munanan hadurran ababen hawa a tituna ya zama ruwan dare a Mexico, galibi saboda tsananin gudu, rashin ingancin motoci ko gajiyar direbobi.
Haka kuma harurran motan da suka hada da manyan motocin dakon kaya ya karu a manyan titunan kasar.
A daya daga cikin hadurran mafi muni da aka yi a shekarun baya-bayan nan, akalla mutane 29 ne suka mutu a watan Yulin shekarar 2023, lokacin da wata motar fasinja ta kauce daga kan titin tsaunuka kuma ta fada cikin wani rafi a jihar Oaxaca da ke kudancin kasar.
A watan Nuwamba, mutane 12 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wata mota ta kife a jihar Veracruz da ke kudu maso gabashin kasar.
Masu fafutukar tabbatar da tsaro sun yi kira da a tsaurara ka'idojin tuki. Hadurra motoci na kan gaba wajen haifar da mace-macen da ake samu a tsakanin bakin hauren da ke yin balaguro zuwa Amurka.
A watan Disamban 2021, mutane 56 akasari bakin hauren Amurka ta tsakiya ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata lokacin da wata motar masu safarar mutane ta kife a jihar Chiapas da ke kudancin kasar.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata wata motar bas da ke dauke da bakin haure ta kife kan wata babbar hanyar da ta hada jihar Oaxaca da ke kudancin kasar da makwabciyarta Puebla, inda akalla mutane 18 suka mutu.