Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 25 A Jihar Neja


Hadarin Mota
Hadarin Mota

Wata babbar mota dauke da kayan abinci da mutane sama da 200 ta yi hatsari a jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya, inda ta kashe fasinjoji 25 tare da raunata wasu da dama, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Laraba.

WASHINGTON, D. C. - Motar dai na kan hanyarta ne ta zuwa cibiyar tattalin arzikin Najeriyar lokacin da ta yi hatsari a kauyen Takalafia da ke gundumar Magama, a jihar Neja a ranar Talata, kamar yadda hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya ta bayyana.

HATSARIN MOTA
HATSARIN MOTA

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kai mutanen 25 da suka mutu zuwa dakin ajiyar gawa da ke kusa, yayin da wasu fasinjojin ke jinya sakamakon raunukan da suka samu.

Kumar Tsukwam, kwamandan sashen kiyaye hadurra na Najeriya a Neja, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, an yi imanin wasu fasinjojin sun so tafiya da tirelar ne cikin daren ranar Talata, don guje wa hanyoyin da ba su da tsaro da rana.

Sabon gwamnar Jihar Neja
Sabon gwamnar Jihar Neja

Daukan kayan da wuce gona da iri yawan gudu nahaifar da hadarurruka a manyan tituna a Najeriya, inda galibi ba a bin ka'idojin zirga-zirgar ababen hawa, inda kuma direbobin da ke kin bin ka'idar sukan kaucewa hukunci.

Hukumomi za su tabbatar da cewa “an gabatar da hukunci mai tsanani ga masu keta dokar hanya” a jihar Neja, in ji Bago.

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma bukaci matafiya da su rika tuka mota a cikin natsuwa, musamman a lokacin da bukukuwan hutu ke kara gabatowa.

"Shugaban kasar ya bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici, kuma ya umurci hukumar da ke da alhakin kai daukin gaggawa da ta gaggauta shiga tare da tabbatar da cewa wadanda suka jikkata sun samu kulawar da ta dace," in ji ofishin Tinubu a cikin wata sanarwa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG