Mutane 11 Sun Rasa Rayukansu A Hari Kan Masallaci A Kano

Masallacin da wani matashi ya cinna wa wuta a Larabar Abasawa

Ana zargin wani matashi, Shafi'u Abubakar, wadda aka ruwaito  cewar,  ya bayyana wata dadaddiyar takaddamar rabon gado a matsayin dalilinsa na haddasa fashewar.

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukkansu fashewar daya auku jiya a kauyen Larabar Asabawa a karamar hukumar Gezawan jihar Kano.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ce ta tabbatar da rasuwar mutanen.

Ana zargin wani matashi, Shafi'u Abubakar, wadda aka ruwaito cewar, ya bayyana wata dadaddiyar takaddamar rabon gado a matsayin dalilinsa na haddasa fashewar.

Ku Duba Wannan Ma Fashewa A Wani Masallaci A Kano Ta Jikkata Fiye Da Mutane 30, An Kama Wanda Ake Zargi 

A cewarsa, “ya aikata aika-aikar ne domin nuna adawa da wata dadaddiyar takaddamar danginsa akan rabon gado, kuma yayi haka ne domin a saurare shi.”

Fashewar ya raunata kimanin mutane 3o, kuma al’amarin ya faru ne da misalin karfe 5 da mintuna 20 na safiya yayin sallar asubahi.

HOTUNA: Masallacin Da Wani Matashi Ya Cinna Wa Wuta A Kano

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace sakamakon binciken farko-farko ya nuna cewar man fetur ne ya sabbaba fashewar.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Mazauna Larabar Abasawa Suka Koka Kan Hari A Kan Masallaci