Al'umman Jukun da Hausawa da ma Fulani sun sha fama da rikici tsakaninsu a garin Wukari da kewaye. Sau da yawa rikicin kan rikide ya zama na kabilanci da na addini.
Wasu sun yi yunkurin magance matsalar albarkacin bikin kirsimati. Wani mai bishara ya yiwa musulmai gayyatar cin abincin kirsimati a gidansa inda su kuma suka amsa.
Sanusi Yusuf yace sun godewa Allah domin an yi bikin cikin lumana da kwanciyar hankali. An yi shagulgula an gayyaci mutane da dama. Yace wani abokinsu ya gayyacesu gidansa. Sun amsa kuma sun ci sun sha tare ba da wata matsala ba. Yace da ma can suna zaune tare basu saba da tashin hankali tsakaninsu ba. Tsautsayi da wasu abubuwan da basu san dasu ba suka faru har suka shiga hargitsi lamarin da ya kaiga rabuwa da zama wuri daya.
Cin abincin da suka yi tare ya kara kawo fahimtar juna tsakanin mabiya addinan biyu. Anguwar da suka ci abinci anguwa ce da musulmi bai isa ya shiga ba amma sai ga bikin kirsimati ya kawar da wannan rabuwar.
Mai Bishara Jethro Agaba wanda ya yi gayyatar yace yayi farin ciki sosai domin ya dade yana neman irin wannan damar. Amma sai ranar kirsimati ya samu ya hada kan musulmai da kiristoci sun zo gidansa sun ci tare sun kuma sha tare.
Abun da ya faru ya nuna cewa komi ya faru musulmai da kiristoci ba zasu iya rabuwa ba. Dole su zauna tare domin 'yanuwan juna ne. Abun da yakamata a yi yanzu shi ne inda suka yi kuskure su gyara domin a tafi tare.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5