Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Francis Ya Tunatar da Mabiya Darikar Katholika Sakon Allah na Zaman Lafiya


Papa Roma Francis
Papa Roma Francis

Yau take Kirsimeti

A jajiberen Kirsimeti jiya laraba, Papa Roma Francis yayi kira ga mabiya darikar katholika su milyan dubu daya da dari biyu a fadin duniya su tuna cewa sakon Allah na zaman lafiya yana da tasiri "kan duhu da kuma rashin gaskiya."
Dubban mutane ne suka hallara a maja'iman nan da ake kira St Peters Basilica a daren jiya laraba, domin su saurari Papa Roma ya jagoranci addu'ar shigar kirsimeti. Ya yi kira ga kiristoci su kimtsa rayuwarsu ta yadda Allah zai albarkacesu , ya kara jaddada cewa duniyar yau tana bukatar kulawa da tausayi.
Kamin ya jagoranci addu'o'in , Papa Roma ya kira kiristoci tav woyar tarho wadanda suke wasu sansanonin 'yan gudun hijira a Iraqi.
Ya gaya musu cewa "yau suna nan kamar Yesu Almasihu a daren kirsimeti. Shima ya rasa muhallinsa, tilas yayi gudun hijira zuwa Masar domin ya tsira da ransa".
'Yan gudun hijiran suna neman tserewa ne daga mayakan sakan ISIS wadanda suke cin zarafin musulmi 'yan shi'a, da kiristoci da kuma wasu a kasashen Syria da Iraqin.

XS
SM
MD
LG