Malaman addinin Kirista sun yi kira ga jama’a da su yi watsi da dabi’u marasa amfani; su rungumi masu fa’ida saboda a sami zaman lafiya cikin al’umma. A hudubobinsu na Kirsimeti, da wakiliyarmu a Jos Zainab Babaji ta aiko, Malaman addinin Kirista din sun ce gudanar da rayuwa kamar yadda Allah ya ce a yi ne kadai zai kawo karshen matsaloli.
Reverend Bitrus Audu Shugaban Majami’ar Christ Ministry Outreach ya yi nuni da cewa ana wa Yesu Kristi lakabi da Sarkin Salama, don haka ya kamata lokacin Kirsimeti ya zama lokacin jaddada zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya ce idan mutane su ka zamanto masu wannan akidar, to za a samu cigaba sosai a fannoni daban-daban na rayuwa.
Shi kuwa Pastor Solomon Garuza Ubasi na Majami’ar ECWA Seminary da ke Jos y ace ya kamata a san cewa a kullum shaidan na kokari ne ya shiga fagen da ba nasa ba don ya haddasa husuma. Don haka, in ji shi, kamata ya yi mutane su yi watsi da zugin shaidan musamman a lokaci irin wannan na Kirsimeti, don a samu cigaba.
Shi kuwa Reverend Thomas D Lot na Majami’ar COCIN LCC, ya ce ya kamata duniya ta yi na’am da akidojin Yesu don ta sami cigaba. Saboda Yesu salama ya jaddada kuma ya zo ne don ceton duniya.
Shi kuwa Dr. Yusuf Turaki wanda ya bayyana kansa a matsayin malami a makarantar addinin Kirista Jos ECWA Theological Seminary ya ce ya kamata a yada sakon zaman lafiya da kuma watsi da rayuwar da ba ta dace ba. A yada rayuwar da’a.
Wakiliyarmu Zainab Babaji ta ce Musulmi sun yi ta aikawa da sakon fatan alkhairi ga Kirista.