Tuni ma dai shugaban kwamitin labarun majalisar Sanata Aliyu Sabi, yace ba ayi kiran bisa manufa mai kyau ba ne, in za a tuna kotun koli ta ‘ki amincewa da bukatar Sanata Bukola kan hana kotun da’ar ma’aikata ci gaba da yi masa bincike kan mulkin sa tun yana gwamnan jihar Kwara.
Masu tunanin ko Saraki na dagewa kan zama a kujerar shugaban Dattawa ne don ya kara karfi don ya nemi shugabancin Najeriya a shekara ta 2019, wannan batu ba gaskiya bane, inji mukarrabin Sarakin Sanata Isa Hamma Misau, har ma yace su shugaba Buhari suke marawa baya.
Mukaddashin shugaban kwamitin amintattun PDP Sanata Wali Jibrin, yace zasu tsayar da dan takarar su daga Arewa a shekara ta 2019, don fuskantar APC. Yana mai nuna farin jinin PDP ma ya fara dawowa.
Duk da dai riga mallam masallaci ne batun zaben 2019, ga masu niyyar takara ko marawa wani baya amma tuni siyasar Najeriya ta fara tafiya da batun wannan zaben. Zuwa yanzu dai shugaba Buhari na dagewa ne kan yaki da wadanda ake zargi sun karkatar da kudin sayen makamai fiye da dala miliyan dubu biyu, kuma babu alamun yana nuna alamar neman zarcewa.
Don karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5