Rahotanni daga jihar Kebbi sun yi nuni da cewa har yanzu al’umar yankin Zuru ciki har da garin Sakaba da Fakai na ci gaba da zaman dar-dar sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin ‘yan sa-kai da barayin daji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sa- kai sama da 50 kuma barayin ma suka rasa wasu mutanensu.
Mazaunin garin Faikai, Umar Muhammad ne ya shaida hakan inda ya ce kisan 'yan-sa kai ya sanya zullumi cikin al’umma da ke ganin an rage adadin wadanda ke kokarin kare su daga miyagun iri da suka addabi garin nasu a halin yanzu.
A cewar sa, a ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan sa kai suka sami labarin cewa barayin daji na kokarin shigowa karamar hukumar Sakaba sai suka yi gangami suka hada kai da sauran ‘yan uwansu a kananan hukumomi 3 ciki har da Fakai, Danko Wasagu, Zuru da kuma karamar hukumar Rijau na jihar Neja suka shiga Sakaba daga nan suka shiga daji.
Lamarin dai ya kai ga musayar wuta tsakanin ‘yan sa kai da barayin dajin inda 'yan bindigar suka kashe 'yan sa-kai da dama sai dai su ma sun rasa wasu ‘yan uwansu, in ji Umar Muhammad.
Har yanzu ba’a a sami cikakken bayani kan adadin ‘yan fashin daji da aka kashe ba sai dai rahotannin sun yi nuni da cewa ba bu mutanen gari da suka rasa ransu.
Tun farkon watan Febrairun ne ‘yan garin Sakaba suka fara kokawa kan kafaffen sada zumunta cewa 'yan bindiga na kashe mutanensu amma ba’a yada labarin inda suka zargi gwamnati da yin halin ko’in’kula da ran mutane da ake kashewa in Ji Umar Muhammade.
A wani bangare kuwa, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zuru, Fakai, Danko/Wasagu da Sakaba, Hon. Kabir Tukura ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya yi Allah wadai da aika-aikar inda ya ce suna duk mai yiyuwa wajen jan hankalin jami’an tsaro zuwa yankinsu su kara hobbasa wajen tsaro rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan ‘yan sa-kan a garin na Sakaba inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiyuwa wajen kawo karshen matsalolin tsaro a yankin da ma Najeriya baki daya.
Ko a ranar Talata ma sai da aka sami rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun kashe jami'an tsaro da dama a yayin wani hari da suka kai wa ayarin motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanar Samaila Yombe Dabai mai ritaya a lokacin da ya ke kan hanyarsa na komawa gida daga karamar hukumar Danko-Wasagu don yiwa al’ummar garin jaje kan harin 'yan bindiga na baya-bayan.