Muna So Danbaba Suntai Ya Koma Jinya - inji Majalisar Dokokin Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Majalisar dokokin jihar Taraba ta fito da matsayar da zata bar mukkadashin gwamnan Alhaji Garba Umar ya cigaba da rike kujerar gwamna.
Da alamu an soma samun mafita game da dambarwar siyasar jihar Taraba, inda majalisar Dokokin jihar yau ta fito da wata matsaya mai cewa Gwamna Danbaba Suntai, ya koma Amurka ya karashe jinya, shi ko mukadashin gwamnan Alhaji Garba Umar ya cigaba da rike kujerar shugabanci a wannan jiha.

Gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai wanda ya kwashe watanni goma yana jinya a kasashen waje ya koma Najeriya ran 25 ga watan Agusta.

Kimanin watanni goma ke nan, gwamnan yayi hadari da jirgin sama wanda shi ne matukin kafin ya sauka a filin saukan jirage dake Yola lamarin da yayi sanadiyar mugun rauni da ya samu.

Da farko an kaishi kasar Jamus inda ya soma jinya kafin a gangara dashi zuwa Amurka.

Tun lokacin da ya soma jinya akai ta kai ruwa rana kan ko zai iya ma komawa Najeriya.


Gwamna Suntai ya sauka a birnin Abuja babban birnin tarayya Najeriya, inda 'Yan jarida suka yi ta kokarin samun zantawa da shi amma duk kokarinsu ya cutura.

Jami'an gwamnati da jami'an tsaro sun mamayeshi suka hana kowa ya yi magana da shi.

Sai dai wakilin Muryar Amurka da ya je kusa ya ce bisa duka alamu gwamnan baya iya tafiya sai da taimako.

Bayan ya sauka a Abuja sai ya shiga wani jirgin da ya kaishi Jalingo. A Jalingon ma bata sake zani ba domin ba'a bari ya zanta da 'yan jarida ba.

Jami'an tsaro sun kankane wuri suka sa shi a mota sai fadar gwamnatin jihar.

Your browser doesn’t support HTML5

Muna So Danbaba Suntai Ya Koma Jinya - 3:04