Mataimakin shugaban kungiyar ta kwadago Tommy Etim, ya bayyana cewa, a baya sun nemi gwamnati ta biya mafi karancin albashi Naira Dubu 200, amma yanzu sun bar wancan turba. A cewarsa yadda yanzu rayuwa tayi tsada a kasar, kamata yayi albashin ya dara haka.
Etim, ya bayyana haka ne a ranar Talata, bayan mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kaddamaar da kwamitin sake duba fasalin albashin ma'aikata a kasar.
Tommy Etim, ya ce "darajar Naira ta fadi, kuma hakan yasa farashin komai ya tashi a kasar, dan haka baza mu lamunci dubu 200 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba".
Etim, ya kara da cewa, " kamata yayi a biya mafi karancin albashi a kasar Dalar Amurka 300, ko kuma Naira dubu 440,000, Etim ya ce wannan shine matsayar su, kuma shi zasu gabatarwa komitin sake duba fasalin albashi da fadar shugaban kasa ta kafa".
Shin ko yaya 'yan Najeriya suka ji da wannan ikirari na kungiyar kwadago na a biya mafi ƙarancin albashi Naira dubu 400.
A hirarsa da Muryar Amurka, Dakta Abdullahi Kashere, masani kuma malami a Jami'ar Tarayya da ke Kashere Jihar Gombe, ya bayyana cewa, gwamnati zata iya biyan mafi karancin albashi Naira dubu 400, ganin cewa, yadda kudaden shigar gwamnati ya karu bayan cire tallafin man fetur da Shugaban Tinubu yayi.
Yanzu dai hankulan 'yan kasar ya karkata ga kwamitin da fadar Shugaban kasar ta kafa na sake duba fasalin albashin a kasar.
Saurari rahoton Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5