A hirarshi da Muryar Amurka, Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya ce dokar kasa da ta hana halasta kudaden haram ta kuma kayyade cinikayya da mutum zai iya yi da kudi tsagoransu, idan mutum ya yi ciniki da ya wuce Naira miliyan biyar lokacin guda sai shine idan mutum ne, idan kuma kamfani ne Naira miliyan goma, duk wannan doka ta kasa tana nan.
Bawa ya ce duk wanda yake so ya yi ciniki fiye da haka idan dai tsagwaron kudin ne ba’a yadda da wannan ba, doka na nan mutum na iya yin gidan fursina, dole sai yaje ta sha’anin banki. Ga wadanda ke sayen kadarori da wadanda ke sayen kayan abinci, wannan Najeriya kasan tana da fadi tana da yawa, ba wanda zai hana mutum yaje ya sai kadara.
Bawa ya kara da cewa “ idan zaka sayi kadara ka biya kudi tsagwaronsu to ai wannan da ya karbi kudin tsagoransu ba zasu yi masa amfani ba sai ya kawo kudadenan a banki, dama muna nan muna aiki sau da kafa tare da mutanen banki, duka bankunan Najeriya da kuma bankin koli muna nan zamu gani.Menene kake kawowa a banki tun can da, da kuma menene ka kawo a yanzu, don karshenta idan wannan abun ya kare, muna son mu gani shin wanene ya saka kudi kaza na kaza, kamar yadda muka fara gani yanzu kuma ko jiya na samu rahoton wanda ya nuna cewa ga mutane wadanda suka saka biliyoyin kudi a asusunsu, ba wanda ya ce karka saka kudinka a asusun banki ba laifi ba ne, muna son mutane su kawo kudadensu su saka a banki.”.
Da yake amsa tambaya kan yadda wasu ke rarraba karfi sai su rarrabawa mutane da yawa kudaden da yawa su je su kai banki domin su basu wani kaso don dai a batar da wadannan kudaden, Bawa ya ce “duk wanda aka ba kudi ya je ya sa kudadenshi a banki hukumar haraji ita ma muna aiki da ita, ita ma zata zo ta tambaya, to ka sa wannan kudin a asusunka ke nan kai mai kudi ne, baka biya haraji kaza ba, ta kowace hanya dai duk wanda yasa kansa yaje aka yi amfani da shi don a tura kudade banki to fa hukumomin Najeriya suna nan suna gani kuma za su yi wani abu a kai.
Bawa ya ce mutanen da suke fuskantar matsalolin tsaro a yankunansu basa ajiye irin wadannan kudade masu yawa na fitar hankali irin wadannan da suke maganganu a kai, ana cewa akwai kudade hannun jama’a tiriliyan 2.7, ba shi ba ne, duk wadannan an san da matsalolin nasu kuma suna iya zuwa bankunan da ke kusa da su, suje su saka wadannan kudaden nasu da kuma wuraren da aka bude na yin wannan.
Saurari hirar cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5