Kasashe da dama ciki har da Amurka, sun yi wa Najeriya tayin taimakawa wajen ceto daliban Kuriga da aka sace a jihar Kaduna, in ji Ministan yada labarai Mohammed Idris.
A karshen makon da ya gabata ‘yan bindiga suka far wa makarantar firaimre da saakandare ta Kuriga suka kwashe dalibai sama da 250 a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
A cewar Idris, gwamnati “na nazari” kan tayin da kasashen suka yi na taimakawa wajen ganin an kubutar da daliban.
Gwamnatin Amurka a cewar AFP, ba ta tabbatar da batun tayin yi ba kuma ba ta yi karin haske a kai ba.
Makarantar firaimare da sakandare ta Kuriga a jihar Kaduna (Hoto: AP)
Kalaman Ministan na zuwa ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ba.
‘Yan bindigar da suka sace daliban sun nemi a biya su Naira biliyan daya a matsayin kudin fansa.
Matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta zama babbar matsala musamman a arewa maso yammacin Najeriya inda ‘yan bindiga kan yi garkuwa da mutane da dama ciki har da kananan daliban makaranta.