Duk Wanda Ya Ga Ba A Yi Masa Adalci Ba A Zabe Ya Je Kotu, Maimakon Tada Jijiyar Wuya- Matasan Kirista 

Matasa Kiristoci

Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen matasa a arewacin kasar ta bukaci duk mabiya su kwantar da hankalin su biyo bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.

Reshen kungiyar ya ce akwai mabiya da ba su ji dadin sakamakon ba bisa zargin ba a yi adalci a zaben ba, amma ya ce ba a samun nasara ta hanyar fito-na-fito.

Shugaban matasan Pastor Musa Misal, ya ce duk da cewa da yawa basu goyi bayan APC kan tsaida dan takarar shugaban kasa musulmi kuma mataimakinsa musulmi ba, yin zanga-zanga ko furta kalamai marasa dadi ba sune hanyar samun maslaha ko maganin lamarin ba. Ya kara da cewa idan akwai matakin da ya dace a dauka ga wadanda basu gamsu ba to kotu ce.

Evangelist Misal ya kuma ce kungiyarsu ta hada hannu da mutane daga sassan arewacin Najeriya dabam-daban a lokacin zaben don kawo zaman lafiya a kasa, amma abin mamaki shi ne a wasu wurare da ba a yi zabe ba a jihar Neja, an samu sakamakon zabe.

Da ya ke sharhi kan batun, mai sanya ido kan harkar zabe Sama'ila Sifawa, ya ce ya kamata a daina duba addini da kabilanci wajen zabe, amma duba cancanta shi ya fi a'ala a Najeriya.

Game da batun nuna kabilanci wajen raba mukamai, Sifawa ya ce idan aka ga Tinubu ya fifita yarbawa a fadar Aso Rock ba sabon abu ba ne idan aka duba gwamnatin da ke kan gado.

Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Muna Goyon Bayan Duk Wanda Ba A Yi Wa Adalci Ba A Zabe Ya Je Kotu - Matasan Kirista