Mun Kaddamar Da Gidauniya Don Ceto Ilimi Daga Durkushewa Bayan Illar Boko Haram-Gwamnatin Yobe

Gwamna Mai Mala Buni

Gwamnatin jihar Yobe ta kaddamar da wata gidauniya don ceto lamuran ilimi daga cigaba da durkushewa bayan fama da illar Boko Haram.

Gwamnan jihar Mai Mala Buni ne bayyana haka yayin jawabinsa ga kwararru, gwamnoni da sauran masu tallafi a taron kaddamar da gidauniyar a Abuja.

Gidauniyar da za ta zama mai zaman kan ta da taken YETFUND” za ta rika tabbatar da daukar kwararrun malamai, gina makarantu da samar da kayan koyarwa ga musamman yara ‘yan firamare.

Hakanan gidauniyar za ta rika duba yaran da ba su shiga makaranta ba don jawo hankalin su ko na iyayen don ilmantar da su.

Mai taimakawa gwamnan jihar na musamman kan ilimi Dr.Kole Shetima ya ce shirin zai tallafawa har da makarantun tsangaya.

A na sa karin bayanin, dan kwamitin shirya gaidauniyar Yusuf Yusufari ya ce za a kafa ofisoshi da mutane za su iya mika bukatar kawo mu su dauki ta fuskar raya ilimi.

Cikin wadanda su ka halarci taron da Sanata Uba Sani daga Kaduna da ke shawartar jihohin arewa su ware kaso mai tsoka don raya ilimi.

Masana a taron sun ba da kididdigar akwai fiye da yara miliyan 10 da ba a saka su a makaranta ba, kuma kashi 90% duk a arewa su ke.