Mun Gamsu Da Matakan Tsaro Da Gwamnati Ke Dauka - Dattawan Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa ta musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yayata, na cewar tana kushe matakan da aka dauka na rurrufe al'amura, a zaman wata sabuwar hanyar yaki da 'yan bindiga a jihohin Arewa maso yamma.

A wata tattaunawa da Muryar Amurka, kakakin kungiyar Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya ce sun fi kowa farin ciki da wadannan dokokin, illa dai sun ba da shawara ne kan yadda ya kamata a yi domin kada su kara haifar da kunci ga jama'a jihohin.

Ya ce matakan da aka dauka suna da muhimmanci shi ya sa suka saki sa’ida cewa ba zai yi wu ba a hana wannan mataki da aka dauka, bai kamata ba sai da ma a yi addu’a ubangiji ya sa a yi sa’a.

Ya kuma kara da cewa sun sa wa matakin albarka da goyon bayansu ba kamar yadda wasu suke nuna cewa ba su yi ba.

Ya kara da cewa, dole ne a sa ido domin dama an daura wa mutane takunkumi sannan hukuma ta kara nata saboda matsalar rashin tsaro, amma sun fahimci niyyar gwamnati suna fatan idan an dauki wadannan matakai za a yi kokari a takaita su.

Saboda hakan, gwamnatin tarayya ta shigo da karfinta don bin inda mutanen nan suke a yi maganin su kada a bar mutane cikin wahala da rashin tsira ta kowane mangare tsakanin wahalar da suke ciki da kuma ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Saurari hirar cikin sauti daga Murtala Faruk:

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Gamsu Da Matakan Tsaro Da Gwamnati Ke Dauka - Dattawan Arewa