Bayan babban zaben shugaban kasa a Najeriya, kungiyoyin matasa da dama a fadin kasar sun taka rawar gani musamman ta wajan fadakarwa da kuma fitowa domin nuna ra’ayin su da kuma yin zanga zangar lumana domin nemarwa kansu ‘yanci.
Ibrahim Garba Wala na kungiyar matasan arewacin Najeriya mai suna National Consensus Movement, ya bayyana cewa kungiyoyin matasa sun taka rawar gani wajan tabbatar da wanzar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben.
Yayin da tsohuwar gwamnati ta dage zaben kasar, kungiyoyin sun nuna rashin amincewar su da wannan lamari. Bugu da kari, kungiyoyin sun yi tattaki da zanga zangar lumana a wurare daban daban dangane da daliban ‘yan matan cibok da aka sace.
A hirar su, matashin ya kara da cewar sun koyi darussa da dama musamman ta wajan wanzar da zaman lafiya a tsakanin matasa da kuma canza tunanin sun a yin shiru, wato yanzu lokaci ya canza da zama shiru na daya daga cikin dalilan da suka sa kasar cikin halin da take ciki yanzu.
Idan muka koma bangaren abinda ke faruwa a kasar Afirka ta kudu, wato yadda ake musgunawa ‘yan Najeriya mazauna kasar, matasa na shirye shiryen yin wani gangami na nuna rashin jin dadin abin da kuma kira ga gwamnati da lokaci yayi ta shiga tsakani.
Your browser doesn’t support HTML5