Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa

Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa

Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa a karkashin jagorancin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ta ce ta amince da dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, domin Jam’iyyar ta nuna adalci wajen tsayar da mataimakin ‘dan takara Kirista.

ABUJA, NIGERIA - Kungiyar ta ce kwamitinta na fasaha ya dauki lokaci yana nazari akan manyan 'yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023. Amma masu fashin baki a al'amuran yau da kullum na ganin bai kamata a hada addini da siyasa ba.

Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa

Kama daga Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC da Peter Obi na Jam’iyyar Labour da Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da kuma Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, kungiyar ta yi nazarinsu in ji ta. Ta ce ta na ganin Jam’iyyar PDP ita ce ta dace da manufofin hadin kan kasa a matsayin ba wa kowa dama, kamar yadda Jam’iyyar ta tsayar da Atiku Musulmi kuma mataimakinsa Kirista.

Tsohon Mataimakin Gwamna a Jihar Sokoto, Muktari Shagari jigo ne cikin kungiyar ya ce ba yau aka fara nuna adalci ba.

Muktari ya ce tun a Jumhuriya ta farko a nan Najeriya, kowane lokaci idan siyasa ta shigo, Idan kungiyoyin siyasa za su tsayar da ‘yan takara, suna la'akari da haki na kowa a Najeriya, kuma suna la'akari da irin tsarin zaman mu yadda yake, musulmi da kiristoci, saboda in an lura a duk lokacin aka tsayar da dan takara Musulmi wajibi ne a tsayar mataimakin sa kirista.

Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa

Muktari ya ce an taba samun Firai Minista Musulmi kuma ‘dan Arewa, sannan akwai shugaban kasa Kirista daga Kudu.

Amma ga mai fashin baki a al'amuran yau da kullum na Kungiyar 100 Percent Focus Movement, Labeeb Abdullahi Mahmoud yana mai ra'ayin a rika sara ana duban bakin gatari. Labeeb ya ce kasa tana cikin wani hali a yanzu, kuma ya kamata manya su san zabin wanda ya cancanta shi ne abu mai amfani ga kasar. Labeeb ya ce da su da kwarkwatansu za su fito kuma su zabi wanda ya cacanta.

Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa

Amma ga Madam Joan Mohammed daya cikin jigajigan mata na kungiyar Arewa Elders Consultative Forum ta ce babu yadda za a yi a raba addini da siyasa a Najeriya, domin yin haka ne kadai zai zama an yi adalci a kasar. Joan ta ce ita Kirista ce kuma mijin ta Musulmi ne, ta ce idan an bi wannan salon kasa za ta zauna lafiya. Joan ta ce demokradiyar Najeriya ba ta yi kwarin a tsayar dan 'yan adinni daya a shugabancin kasa ba.

Akwai alamun rarrabuwar kawuna a Kungiyar tuntuba ta Shugabanin Arewa din domin tsohon Sakataren Gwamnati na Kasa, Babachir David Lawal, wanda jigo ne a Kungiyar, ya fito kakafen yada labarai, ciki har da Muryar Amurka, da bayanin cewa shi zai gwammace zaben Jam'iyyar Labour wacce ta tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi da Dokta Yusuf Datti Baba Ahmed daga bangaren Arewa.

Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Amince Da Jam’iyyar PDP Domin Manufofinta Sun Dace Da Hadin Kan Kasa - Kungiyar Tuntuba Ta Shugabannin Arewa.mp3