Wata mummunar guguwa mai sanyi ta lullube galibin gabar gabashin Amurka da dinbin dusar kankara, ta hana mutane fita daga gida, ta sa motoci kafewa, ta kuma haddasa wani yanayi na hazo-hazo, wanda masu hasashe ke cewa ka iya zama mai hadari ga rayuwa.
WASHINGTON, DC —
Ya zuwa yanzu tarin dusar kankara mai hawan Santimita 30 ne ta zubo a sassa daban-daban na yankin, ciki har da Washington DC.
Masu hasashe sun ce al'amarin na iya fin haka ma muni, ta yadda hawan dusar kankarar na iya ribanya, ta kuma hadu da iska mai karfin gaske ta haddasa karin mawuyacin yanayi.
A kalla mutane 9 sun mutu a fadin kasar ya zuwa yanzu sanadiyyar mummunan yanayin, wanda ya haddasa dusar kankara mai hadarin gaske kama daga Georgia zuwa New England.
An kafa dokar ta baci a jahohi akalla 10.