Kasar Amurka tace dole ne China ta hadu da sauran kasashen duniya domin tsawwala takunkumi kan kasar Koriya ta Arewa, kan gwajin makaman Nukiliyar ta na baya bayan nan a saboda irin dangantaka ta musamman da take da ita da Koriya ta Arewa.
Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, shine yayi wannan kira a yau Laraba, a birnin Seoul lokacin wani taro da ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Koriya ta Arewa dai ta batawa sauran kasashen duniya rai, alokacin da ta ce ta gudanar da gwajin bam na hydrogen na farko da ta taba yi ranar 6 ga watan Janairu, duk da cewa tana cikin wasu takunkumin MDD na aikata ire iren wannan gwaji a baya.
China da Koriya ta Arewa abokaine na kut da kut a fannin harkokin difilomasiya da kasuwanci, amma wannan dangantaka tasu ta yi tsami alokacin da Koriya ta Arewa ta kasa yin watsi da burin ta na mallakar makaman Nukiliya.