A yayin da aka shiga goma na tsakiya a azumin Ramadana, Malam Mustapha Yunusa shugaban sashen koyar da ilimin lafiyar al’umma na kwalejin tsafta dake Kano wato School of Hygiene, ya yi bayani akan muhimmancin wanke kayan lambu, da 'yayan itatuwa da sauran kayan marmari.
Malam Mustapha ya ce galibin mutane ba su damu da tsaftace kayan marmari ba kamar su dabino, lemun bawo wanda rashin wanke su ka iya haifar da cututtuka irin su kwalara ko atini.
"Wajibi ne a kula da abubuwan ci ta yadda ba za su lalace da wuri ba ko su janyo rashin lafiya, a cewar Malam Mustapha. Shugaban kwalejin ya kara da jaddada muhimmancin wanke hannu kafin cin abinci.
Ga cikakken rohotin daga Baraka Bashir cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5