A daidai lokacinda shugaban Amurka Donald Trump ke kammala ziyarar kwannaki hudu a kasar Japan, an jadadda muhimmancin Karfafa dangantakar soji tsakanin Amurka da Japan, ganin irin yadda China ke ta kara zabura.
A safiyar yau firai Ministan Japan Shinzo Abe, ya shirya wa shugaba Trump liyafa a cikin wani jirgin ruwa mai suna JS Kiga dake jigilar jirage masu saukar ungulu .
Shuwagabannin biyu basu ambaci kasar China ba, koda yake hankalin su yana kan Beijing din ne, akan matsayinta na soji a yankin.
Shugaba Abe yayi magana akan inganata tsaro a yankin.
Shi kuwa Trump cewa yayi idan Japan zata sayi Karin jirgin yaki kirar F-35 guda 105, akan kudi dala miliyan $100 kowanne jirgi daya, hakan zai taimakawa kasashen wajen kare kansu da ma sauran kasashe.