Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Ranar Farko Na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Na 76

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Taron na wannan shekara ya banbanta da yadda aka saba gani a shekarun baya, inda dubban mutane ke halartar wannan taro dake tattaro shugabannin kasashe da firai ministoci da manyan tawagogi da kuma wakilai na kungiyoyi masu zaman kansu zuwa nan birnin New York.

Matakin takaita yawan masu halartar taron na zuwa ne yayin da duniya ke fama da annobar coronavirus wacce ta yi sanadin soke taron gaba da gaba tsakanin mahalarta a bara.

Kasashen duniya da dama ne suka iso na New York domin gabatar da jawabai a kan halin da kasashen su ke ciki.

Abubuwan da taron bana zai fi maida hankali a kai sun hada ne da batun sauyin yanayi, annobar COVID-19 musamman batun allurar rigakafi da makaman nukiliya da batun Shirin Muradun Karni da kuma raya kasashe masu tasowa.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya aike wa shugabannin duniya wani sako kafin fara taron a a ranar Litinin yana cewa lokaci ya yi da ya kamata mu tunasar da juna cewa muna karkacewa a tafiyar da muke yi, kama daga batun rigakafin COVID-19, batun sauyin yanayi ga kuma yake-yake a cikin ‘yan watannin da suka shude, lallai akwai bukatar canza lale, kuma mu farka daga bacci don haka wannan shi ne sako na.

Batun tabbatar da murandun karni na cikin tarukan da aka gudanar ranar Litinin, wanda Antonio Guterres ya bukaci mahalarta taron su bada hadin kai ga gwamnatocin kasashen, domin aiwatar da shirin da zai farfado da duniya daga wannan annoba ta coronavirus.

Ya ce duniyar mu ta shiga cikin wata matsalar da ba a taba ganin irin ta ba, kama daga sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da annobar COVID-19, matsalolin da ke kawo cikas ga shirin na muradun karni, wannan zai iya sa a karaya, amma dai ba zamu karaya ba kana zamu taimaka wa juna idan muna son yin hakan.

Firai ministan Burtaniya Boris Jonhson

Yayin da ya ke jagorancin tattaunawa a kan sauyin yanayi a ranar Litinin, firai ministan Birtaniya, Boris Johnson, ya ce dole ne kasashe masu karfin tattalin arziki su tara dala biliyan $100B domin aiwatar da shirye-shiryen dakile barnar sauyin yanayi idan har ana son a kawo karshen barnar sauyin yanayi.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Johnson ya nuna takaicinsa a kan yadda kasashe masu tasowa ke fuskantar tsananin barnar da sauyin yanayi ke haddasawa a duniya.

Johnson ya ce kasashe masu tasowa ne ke fuskantar manyan kalubaloli da sauyin yanayi ke haddasawa, kama daga manyan guguwa da wutar daji da ambaliya ruwa da kuma rushewar tattalin arziki, alhali kuwa manyan kasashen duniya ne ke gurbata yanayi kusan shekaru 200.

Wani taro kuma da hankali ya karkata aakai shine wanda aka yi a kan batun makamashin atomic da ake kera makaman nukiliya da shi.

Babban darektan hukumar sa ido a kan makaman nukiliya, Rafael Mariano Grossi, ne ya jagoranci tattaunawar, inda ya yi alkawari cewa, ina sa ran nan bada dadewa ba zan je birnin Tehran a kan wadannan muhimman batutuwa domin tabbatar wa duniya babu wata damuwa kana kuma a bude wani shirin diflomasiyya da ake bukata da kowa zai yi na’am da shi.

Kamar yadda aka saba gani an jibge jami’an tsaro da dama a birnin New York domin bada kariya da tsaro ga baki da suka shigo kasar Amurka domin halartar wannan taro.

Your browser doesn’t support HTML5

MUHIMMAN TARUKA A RANAR FARKO NA MDD