Dukan jami’iyun Najeriya sun kammala zabukan fidda wadanda zasu yi takarar shugabancin kasar a shekarar badi.
Bisa ga bayanai da kuma muhawara da ake yi tsakanin al'umma, addini yana da gagarumin tasiri a zaben shugabannai a Najeriya a bana fiye da kowanne lokaci a tarihin damokaradiyar Najeriya.
A hirar shi da Muryar Amurka, Sheikh Muhammad Nuru Khalid yace Najeriya na bukatar wadanda zasu hada kan ‘yan kasar ne.
Shima a nashi bayanin, Rabaran Stephen Panya-Baba yace ya dace a sami mabambantan addinai a shugabancin Najeriya don tabbatar da adalci.
Tsohon Ministan sadarwa a Najeriya, Ibrahim Dasuki NaKande yace duba da irin matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, kasar na bukatar jajirtattun shugabannai ne, ba tare da la’akari da addinansu ba.
Malam Salis Muhammad Abdulsalam dake aikin wanzadda zaman lafiya a Najeriya yace samun ilimin addini da na boko zasu taimaka wa ‘yan kasar fita daga kangin jahilci da mafi yawan al’ummar kasar ke ciki.
Al’ummar Najeriya dai na fatar samun shugabannai ne da zasu kawo canji mai amfani ga zamanta kewarsu, dakile matsalolin tsaro da sawwake hauhawar farashin kayan masarufi da sauran matsaloli.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5