‘Yan takarar shugaban kasar Amurka su biyu da suka hada da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da Sanata Banie Sanders sun tafka muhawara a daren jija a birnin Milwuaukee na jihar Winscosin, yayin da salon yakin shiga fadar White House ya dauki sabon salo.
WASHINGTON, DC —
A wani lokacin nan baya ansa rai cewa Hillary ce zata samu tutar tsayawa takara.
Amma kuma sai gashi a zaben farko na share fage wanda aka yi a Iowa da kyar tasha a hannun Banier Sanders, yayin da kuma tasha kashi a zaben jihar Hamspshire.
Shi dai Banier dan jamiyyar ne na Democrat mai ra'ayin sassauci, kuma ya samu yawancin kuri'un sa ne daga matasa.
Sai dai babban kalubalen dake gaban sa shine ganin ya ci gaba da rike wannan nasarar.
Haka ita ma Clinton ta samu goyon baya daga asusun tallafawa na ‘yan bakaken dake wakiltan Amurkawa masu launin bakar fata.
Yanzu dai akwai kallo a zaben sati mai zuwa wanda za’ayi a South Corolina wanda dukkan ‘yan takarar sun yi kanfe sosai.