Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwagwarmayar Zaben Fidda 'Yan Takara A Amurka


Democrats gather for their caucus, West Des Moines, Iowa, Feb. 1, 2016. (K. Farabaugh/VOA)
Democrats gather for their caucus, West Des Moines, Iowa, Feb. 1, 2016. (K. Farabaugh/VOA)

‘Yan takarar shugaban cin Amurka Sanata Banie Sanders shi da mashahurin mai kudin nan Donald Trump, sun samu gagarumar nasara a cikin jamiyyun su a zaben da akayi a jihar New Hamspshire.

Yanzu kuma hankali ya koma a jihohin South Carolina da Nevada.

Sanata Sanders dai ya doke abokiyar karawar sa ce tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da maki 60, yayin da ita kuma ta samu 38. Haka shima Donald Trump ya samu kashi 35 inda ya kusa ninka wanda ke biye dashi Gwamnan jihar Ohio John Kasich yayin da ya baiwa sauran ‘yan takaran tazara mai yawan gaske.

Sakamakon wannan zaben na New Hamspshire ya haifar da raguwar ‘yan takaran na jamiyyar Republican domin ko tsohuwar shugaban kanfanin kere-kere Carly Fiona wadda tazo na 7 a jerin ‘yan takaran da gwamnan jihar New Jersey Chris Christie sun bayyana cewa sun janye daga takaran.

Wannan yasa yanzu haka suran ‘yan takaran dake kan gaba sun fara hararen zabe na gaba wanda za ayi mako mai zuwa.

Yayin da jamiyyar Republican zata gudanar da nata a jihar South Carolina ita kuma Democrat zata yi nata a jihar Nevada, jihar Nevada dai it ace jihar da tafi kowace wuraren caca a duk fadin Amurka.

Bayan wannan ne kuma sai bayan kwanaki ukku ita jamiyyar Republican tayi nata zaben nata a jihar Nevada kana Democrat tayi nata a jihar South Carolina a ranan 27 ga wannan watan.

Wannan nasarar da Donald Trump ya samu yasa shi kalaman kaskanci ga sauran abokan hamayyar sa musammam ma dai gwamnanjihar Florida dan tsohon shugaba Bush Jeb Bush wanda yazo na hudu a zaben na New Hamspshire, inda yake bayan Ted Cruz.

XS
SM
MD
LG