Farida Odangi Suleiman ‘yar asalin garin Abaji na birnin tarayya Abuja ce kuma tsohuwar mai taimakawa tsohon ministan Abuja a mulkin shugaba Buhari inda ta ce duk da cewa Allah ne zai yi musu mafita amma suna yin kira ga shugaba Bola Tinubu ya share musu hawaye a yi musu adalci.
Shi ma kwararre a aikin tsara birane wanda ya fito daga karamar hukumar Kwali, TPL Abubakar Sadiq Ahmad, ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta yi kokarin su ‘yan asalin birnin tarayya Abuja su kasance cikin gwamnati, musamman ma cikin majalisar zartarwar kasar tun da su basu da gwamnati a tsakiya kamar sauran jihohi.
Barrister Mainasara Kogo, fitaccen masanin kundin tsarin mulki a Najeriya ya ce idan ana son a yiwa ‘yan garin adalci, kamata ya yi a kara musu yawan kujerun wakilci da suke da su a majalisar dokoki ta tarayya.
A baya-bayan nan, masu ruwa da tsaki ‘yan asalin cikin birnin sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta zartar da wani kudirin doka da zai tabbatar da dunkulewar mutanen babban birnin tarayya Abuja cikin tsarin kananan hukumomi na kasa don samun gajiyar ababen more rayuwa, cigaban tattalin arziki, siyasa da zamantakewa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5