Bayanin na kunshe cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaba kasa Bola Tinubu a kan harkokin na musamman da yada labarai Dele Alake ya fitar ma manema labarai a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, 2023.
Sanarwar ta jaddada cewa shugaba Tinubu bai amince da karin albashin da ake yadawa cewa za’a kara shi har kaso 114 cikin 100 ba, kuma ba a gabatar shugaban kasar wata shawara dangane da wannan batu ba.
Duk da cewa yana cikin ikon tsarin mulki na hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi da kasafin kudi (RMAFC) na gabatar da shawarwari da tantance albashi da alawus-alawus na masu rike da mukamai na siyasa da na shari’a, duk wani sauyi a wannan fanni dole yana bukatar shugaban kasa ya duba da kuma amincewa kafin ya fara aiki.
Abin takaici shi ne yadda ake yada wadannan bayanai marasa tushe a shafukan sada zumunta da kuma wasu sassan kafafen yada labarai na yau da kullum na nuna illar da ke tattare da labaran karya, domin hakan na iya yin illa ga al’umma da kuma ci gaban kasa.
A bayyane yake cewa an ƙirƙira wannan ɓoyayyiyar bayanai ne don haifar da mugun nufi ga sabuwar gwamnati, da kawo cikas ga ci gabanta, da kuma lalata kyakkyawar fahimta da take samu a tsakanin ‘yan Nijeriya a halin yanzu, saboda manufofinta masu kyau na ci gaba.
Itama a bangaren hukumar RMAFC, ta hannun Manajan Hulda da Jama’a, ta mayar da martani kan wannan labari na ƙarya da ake yawo musamman a kafafen sada zumunta da wasu jaridu na kasar, inda hukumar ta jaddada rashin sahihancin labarin mara tushe.
Dele Alake, mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, Sadarwa da Dabaru, ya sake nanata waɗannan batutuwa a cikin sanarwar, yana mai jaddada mahimmancin dogaro da tabbataccen tushe da tashoshi na hukuma don samun bayanai.
A karshe an bukaci ‘yan jarida da su rinka bin diddigin labarai, tantacesu bisa mizani na gaskiya kafin yada su, bugu da kari sanarwar ta jaddada ma manema labarai, manhajojin yada labarai, da jama’a da su yi watsi da labaran da suka shafi ayyukan gwamnati da manufofin da ba su samo asali daga hanyoyin sadarwa na gaskiya da aka amince da su ba.
~ Yusuf Aminu