Mu Hakkin mu Muke Nema a Wurin Gwamnati

Gwamna Jonah Jang

‘Yan Fensho a jihar Filato, sun gudanar da zanga-zangar lumana suna rokon Gwamnati da ta biyasu hakkokinsu da suke bin ta.

Shugaban kungiyar ‘yan fenshon na kasa rashen jihar Filato, Danladi Jimoh, yace dayawan ‘yan fenshon sun mutu saboda rashin abun biyan bukata.

Ya kara da cewa yawancin ‘yan kungiyar na fama da rashin lafiya, da kuma cewa sun yi koke-koke ga Gwamnati, har yanzu shuru, ya cigaba da rokon Gwamnati, da ta dubaisu da idon rahama ta biya masu bukatunsu ko suma zasu samu saukin kuncin rayuwa.

Yana kuma mai cewa zanga-zangarsu bata da wani nasaba da siyasa, su dai hakkinsu suke nema a wurin Gwamnati, abunda yake halaliyarsu ne suke kuka aka.

Shugaban ma’aikatan jihar Filato, Eziekel Daliyop, yayi alkawarin cewa nan bada jimawaba Gwamnati, zata biya su hakokinsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga-zangar 'yan fensho - 3'54"