Shugaba Barack Obama zai tattauna da shugaba Xi Jinping na Sin da Francois Hollande na Faransa a wajen taron manyan kasashe 20 da ake yi a Rasha
WASHINGTON, DC —
A yau jumma’a shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ke shirin ganawa da shugabannin kasashen China da Faransa a wajen taron kolin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki, wanda maganar Syria ta fi daukewa hankali.
A wajen taron kolin na Saint Petersburg, kasar Rasha, Mr.Obama zai tattauna da shugaban kasar China Xi Jinping da kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande.
A yau jumma’a ake kammala taron kolin na kwanaki biyu, wanda kusan duka manyan batutuwan da aka tattauna a kai suka shafi maganar kokarin da Amurka ta ke yi na neman goyon bayan kasashen duniya su kaiwa Syria harin soja.
A wajen taron kolin na Saint Petersburg, kasar Rasha, Mr.Obama zai tattauna da shugaban kasar China Xi Jinping da kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande.