Motoci Kirar Cardillac 17 Muka Ba Sarakuna Ba 230 Ba - Matawalle

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya maida martani kan cece-ku-cen da ya biyo bayan rabawa sarakunan gargajiya a jihar motoci da kuma alakantan sayen motocin da zunzurutun kudin da aka kiyasta cewa ya kai biliyoyin nairori.

ZAMFARA, NIGERIA - Wasu ‘yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu a game da batun raba motocin, inda suka nuna rashin gansuwar da lamarin, amma wasu suna ganin hakan don taimakawa sarakunan ne sabili da rashin tsaro da suke yawan fuskanta.

Tun bayan da labarin raba motoci kirar Cardillac wanda aka kera a shekarar 2019 sama da 200 ga sarakunan gargajiya a jihar Zamfara ya karade kafaffen sada zumunta ne ‘yan Najeriya daga shiyoyin kasar daban-daban ciki har da kudanci kasar suke tofa albarkacin bakinsu a game da lamarin.

Wasu yan kasar dai sun yi ta bada misali ga labarin raba karin motoci ga cibiyar tsaro ta yammacin Najeriya, wanda aka fi sani da suna Amotekun da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi a cikin watan Afrilu inda ake cewa ya ya za’a yi jihar dake fama da tarin matsalolin tsaro ta raba motoci masu tsada ga sarakuna.

Ku Duba Wannan Ma Har Yanzu Ina Cikin Takarar Neman Shugabancin APC-Abdul'aziz Yari

A bayanin sa, gwamna Bello Matawalle ya ce motoci guda goma sha bakwai ne ya raba ba 200 ba, sannan kuma sarakunan da aka baiwa motocin an tabbatar da cewa basa hulda da ‘yan ta’adda kuma suna da mukami da rikon gaskiya, kuma ba abu ne mai kyau ba ace sarakuna irin wadannan basu da motar hawa.

A game da tambayoyi da yan Najeriya musamman a kafaffen sada zumunta suka yi ta yi na cewa shin gwamna Matawalle ya taba taimakon jami’an tsaro a jiharsa da kayan aiki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba El-Kana ya bayyana cewa gwamna Matawalle ya taimaka masu da motocin aiki kuma ya basu goyon baya wajen aikinsu da yaki da ‘yan ta’adda.

Hoton wani mai yada zane-zane a kafar sada zumunta na Instagram ya fi jan hankali inda wasu ke ci gaba da yin tir da raba motocin ga sarakuna wasu kuma na cewa akwai bukata.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Motoci Kirar Cardillac 17 Muka Bai Wa Sarakuna Ba 230 Ba - Matawalle