Kamfanin kera kayayyakin motoci nan mai suna Delphi, wanda a kwankin baya ne ya kera mota mai tuka kanta kirar Audi SQ5 mai kunshe da duk kayan fasaha da ake bukata ga mota mai tuka kanta.
Delphi ya bayar da sanarwar gwada sabuwar motar da ya kera akan hanya kamar sauran motoci.
Motar dai ta dauki kwanaki tara, da tafiyar kilomita dubu uku da ‘dari hudu akan hanya, wadda ta keta jihohin Amurka har guda goma sha biyar kafin motar maras matuki ta gama wannan gwaji.
Domin tabbatar da dokokin tukin Amurka, mutum ‘daya ne ya zauna a kujerar fasinja alokacin wannan tafiya, domin idan an samu kuskure ko akasi mutumin ya karbi akalar tukin. Injiniyoyin kamfanin ne ke lura da duk motsin da motar tayi daga na’ura mai kwakwalwa alokacin wannan tafiya.
Kamfanin Delphi yace kaso casa’in da tara cikin ‘dari na wannan tafiya, motar ce ta tuka kanta.
Alokacin wannan tafiyar dai motar ta fuskanci duk kalubalen tuki na kan hanya, wadanda suka hada da cunkoson hanya, gada, hanyar ‘kar’kashin ‘kasa, harma da sauran direbobi masu tafiyar ganganci akan hanya. Amma duk da haka kwalliya ta biya kudin sabulu, domin motar ta dawo lafiya.