Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 39 A Gidan Yari Batare Da Aikata Laifin Kisa Ba


U.S. Prison
U.S. Prison

An saki wani mutum ‘dan jihar Ohio, dake tsare a gidan yari har na tsawon shekaru talatin da tara, kan laifin kisa da bai aikataba. Kuma za’a bashi sama da dalar Amurka miliyan ‘daya, sama da Naira milayan dari biyu kenan, saboda ‘daure shi da akayi ba tare da ya aikata laifi ba.

Alkalin kotun Ohio ne ya yanke hukuncin cewa a biya mutumin mai suna Ricky Jackson, wanda shine mutumin da a tarihin Amurka ya dade a daure daga baya kuma aka tabbatar da bai aikata lefin ba.

Alokacin da mutumin ya samu labarin cewa kotu ta yanke hukuncin a sake shi kuma a bashi sama da dala miliyan daya, yace wow wow wow, wannan abune mai kyau, ban ma san me zance ba, kuma zai zamo abu mai muhimmanci a gareni.

An dai samu mutumin da wasu mutane uku da laifin kisa a shekara ta alif dari tara da saba’in da biyar 1975, kan kashe wani mutum mai suna Harold Franks.

Wani yaro ‘dan shekaru goma sha biyu ne ya bayar da sheda a kotu cewar yaga lokacin da suka kashe marigayin, yadda takardun kotu suka nuna.

Yaron da yayi shedar a lokacin mai suna Eddie Vernon, ya dawo ya fadawa jami’an tsaro gaskiya cewa shi bai gani da idon sa ba kamar yadda ya fada shekarun da suka shude, kuma babu wata shaida da ta alakanta shi da kisan, in banda yaron nan.

Hakan ne yasa alkali ya bada umarni a sake shi daga gidan yari, a kuma biyashi diyyar tsare shi da akayi ba tare da ya aikata laifi ba.

XS
SM
MD
LG