Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akilu Mohammed (Baban Mulika), Ya Shawarci Matasa Kan Gudanar Da Bukukuwa Cikin Natsuwa


Yusuf Haruna Funtua (Baban Chinedu). Daya daga cikin abokan aikin Akilu Mohammed (Baban Mulika)
Yusuf Haruna Funtua (Baban Chinedu). Daya daga cikin abokan aikin Akilu Mohammed (Baban Mulika)

A cigaba da bayar da shawara ga matasan Najeriya kan muhimmancin gudanar da shagulgulan nasarar zabe cikin natsuwa da kwanciyar hankali, wani shahararren dan wasan barkwanci da ke Kaduna mai suna Akilu Muhammad, wanda ake fi sani da suna Baban Mulkia, ya ce lallai wannan sauyin gwamnati da aka samu ko ake gab da samu a Najeriya abin farin ciki ne, ganin yadda ‘yan Najeriya su ka yi ta wahala a baya. To amma ya yi kira ga matasan Najariya da cewa kai su tsaya kawai ga murnar canjin da aka samu; su ma su canza rayuwarsu saboda kasar ta ci gaba.

Malam Akilu (ko Baban Mulika), ya yi takaicin yadda wasu matasa su ka yi ta gudanar da shagulgula masu cike da hadari har su ka yi ta kashe kawunansu da jijjin raunuka. Ya ce a maimakon a rika gudanar da bukukuwa masu cike da hadari, kamata ya yi a yi taka tsantsan tare da zuwa Masallatai da Majami’u don gode wa Allah.

Ya ce a wani sha tale-talen titin Waff Road da ke Kaduna, wasu masu guje-guje da ababen hawa don murnar wannan zaben, sun hallaka wani yaro mai suna Abdullahi bayan da ya rufe shagonsa za shi gida. Y ace wannan abin takaici ne. Don haka a rika bi a hankali. Ya ce kuma duk wanda ya ce da matasa su je su kone dukiyar wasu, to a ce masa ya sa dan cikinsa ya shige gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG