Mota Mai Tuka Kanta

Mota

Kamfanin fasahohi na sony ya shiga sahun kamfanonin dake rige rigen kera motocin fasaha na zamani.

A wani rahoto da mujallar FT ta fitar, yace fitatcen kamfanin fasahar nan na Sony ya hada gwiwa da wani kamfanin kasar japan mai suna ZMP, domin kera sabuwar mota da zata tuka kanta.

Sony dai ya zuba jarin dala dubu dari takwas da arba’in da biyu $842,000, a kamfanin ZMP, domin hada karfi da karfe wajen shiga gasar kera motocin zamani cikin gaggauwa.

Kamfanin Apple ma nada nashi kudirin kera irin wannan motar, kamar yadda rahotanni da dama da aka fitar a satin daya gabata suka baiyana. Haka kuma kamfanin Google mai shafin bincike na kan yanar gizo, ya yi shekaru yana kokarin kera ire iren wadannan motocin.

Sony dai nada karfi wajen firikwensin hoto, da yake amfani da ita a kamarorin daya kera, zai iya amfani da firikwensin a sabuwar motar da bata da matuki. Saboda ita kanta motar da zasu kera na bukatar kamarori har kusan goma domin nazarin motocin dake kusa.

Ita wannan motar da ita zata tuka kanta, da aka kiyasta cewa za’a fara fitar da ita a shekara ta dubu da ashirin 2020, “kamafanin Sony zai zama na farko dake da firikwensin mota mai kyau,” inji babban manajan kamfani a wata tattaunawa.

#caption:Mota (File Photo)##