WASHINGTON, DC —
A jiya Alhamis ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta APC, janar Muhammadu buhari, yabar babban birnin tarayya Abuja zuwa Ingila.
A wata sanarwa data fito daga daraktan yada labarai na kungiyar kamfen din shugaban kasa Mallam Garba Shehu, tace, “A cikin wannan tafiya da janal Muhammadu Buhari yayi, ana sa ran zai tattauna da wasu kososhin siyasar Birtaniya, kuma zai hadu da masu ruwa da tsaki wadanda ke da sha’awa kan siyasar Najeriya.”
Sanarwar dai ta ci gaba da cewa kila yayi magana ko kuma ya gabatar da jawabi a cibiyar manufofin harkokin kasashen waje, da ake cewa Chatam House da turanci a birnin London.