Sabon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP, Sanata Ali Modu Sharif, ya umarci lauyoyinsa da su gurfanar da tsohon daraktan labarun kamfen din tsohon shugaba Jonathan, Femi Fani Kayode, don tuhumar bata masa suna ta hanyar alakanta shi da Boko Haram.
WASHINGTON, DC —
Sherif wanda yace baya gaba da duk wadanda suka yi adawa da shi wajen neman shugabancin na PDP, amma yace ba zai kyale batun Kayode ba, har sai sunje gaban alkali domin wannan ba siyasa bace a cewarsa.
A nasu bangaren amintattun jam’iyyar sunce ba zasuyi katsalandan da matakan da Sharif din ke dauka ba, wanda suke ganin zai yi mulki ne na kayyadadden lokaci.
Madu Sharif Dai tuni ya fara nada mataimakansa a hedikwatar jam’iyyar, inda tuni ya nada tsohon kwamishinan labarun Borno Inuwa Bwala, a matsayin jami’in labaru, sai kuma Shatima Shehu a matsayin mataimaki kan ayyuka na musammam.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5