Monday Okpebholo Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Edo

Monday Okpebholo

Monday Okpebholo ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP mai mulki Asue Ighodalo.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo.

Monday Okpebholo ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP mai mulki Asue Ighidalo.

Babban jami'in tattara sakamakon zaben gwamnan Edo Farfesa Faruk Adamu Kuta ya bayyana cewa Monday Opebholo ya samu kuri'u 291,667 yayin da Asue Ighodalo ya samu kuri'u 247,274.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar Labour ce ta zo ta uku, inda dan takararta Olumide Akpata ya samu kuri'u 22,763