Babbar kungiyar makiyaya ta Najeriya Miyetti Allah “CATTLE BREEDERS” ta nisanta kan ta daga labarin da ke cewa ta zayyana kashe-kashe a jihar Filato kwanannan da ramuwar gayya da makiyaya su ka yi don yadda a ka zalunce su a baya da sace mu su shanu.
Da ya ke magana a helkwatar kungiyar a Abuja, shugaban kungiyar na kasa Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru ya ce s,am kungiyar ba ta da alaka ta kusa ko nesa da wannan matsaya kuma sam kungiyar ba ta mara baya ga kashe mutane ba gaira ba dalili.
Ardon Zuru ya bukaci jami’an tsaro su zakulo duk wanda ya tada fitina su hukunta shi don kungiyar ba za ta taba mara baya ga zubar da jinin kowa ba,
"Ko ni ne na yi alifi zan ba da hadin kai don a yi mi ni hukunci" inji Ardon Zuru wanda ya bukaci gwamnati ta bincika don gano kungiyoyin Fulani na bogi.
Miyetti Allah wacce ta samu rijista da gwamnatin Najeriya fiye da shekaru 30, tana da hadin kai da sarakunan gargajiya inda Sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar ya ke matsayin shugaban kungiyar.
Saurari rohoton
Your browser doesn’t support HTML5