Jiragen yakin sojojin saman Nigeria sun yi rugurugu da wasu sansanonin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Jiragen yakin sun tarwatsa 'yan bindigan dake yankunan Shinkafi, Galadi, Aja, Gaji Bawar, da sauran wasu wuraren.
Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Nigeria Air Marshal Sadique Abubakar yace aikin 'yan bindigar tamkar yaki ne saboda haka suka yi damarar fafatawa yanzu. Yadda mutane ke daukan manyan bindigogi su shiga gari su soma kashe mutane haka siddan, yaki ne a fahimtarsu.
Dangane da yadda abun dake faruwa a jihar Zamfara ke shafar jihar Katsina dake makwaftaka da ita, gwamnan jihar ta Katsina Alhaji Aminu Bello Masari cewa ya yi mutanen da sojoji ke fatattaka daga Zamfara, suna shigowa jiharsa suna satar mutane da yin fashi da makami.Suna garkuwa da mutane a dazuzzukan na Zamfara sai an biyasu kudin fansa sannan su sako su.
Kamar yadda gwamnan Katsina ya yi bayani kananan hukumomi tara da suka yi iyaka da dajin Zamfara lamarin ya shafa. Kananan hukumomin da lamarin yafi shafa su ne Jibiya, Batsari, Safana, Dan Musa, Kankara da Faskari. Akwai wasu 'yan binidgar kuma a dajin Birbis wanda yake kusa da Zamfara da Faskari da kuma Sabuwa.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5