Yayinda yake jawabi a taron manema labarai a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, daraktan labarai na hedkwatar tsaron Nigeria, Birgediya Janar John Agim, ya ce farmakin Operation Sharan Daji da suke gudanarwa na ci gaba da kawar da 'yan bindiga a jihar ta Zamfara.
Kanar Muhammad Dole kakakin runduna ta daya ta sojojin ya yi karin bayani akan hare-haren da mayakan Najeriyan suka kai. A wani Fermaki da dakarun na Najeriya syuka kai inji Kanal Dole sun yi nasarar kashe manya manyan 'yan bindiga irin su Dan Boko, da Dan Buzuwa wadanda sanannu ne da suka addabi mutane ainun.
Baicin kashe gungun 'yan bindigan, sojojin sun kama babura wajen 36 da wayar hannu wajen 30 da motoci guda biyu. An kwato shanu fiye da dubu daga muggan mutanen, tuni har an mika su ga masu dabbobin. Kazalika sojojin sun kubutar da mutanen da aka sace tare da kudaden fansar da suka karba daga mutane.
Kanar Ahmed Dole ya ce hadin guiwar da su keyi da sojojin sama shi yake taimaka masu. Ayyukan da sojojin saman suka yi a dazukan sububu da rubu, Sune suka ba sojojin damar kustawa inda 'yan ta'addan suke, wadda a baya basa iya shiga. Wannan damar da suka samu ta sa sun hallaka 'yan ta'addan da dama.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum