Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Mayakan Saman Nigeria Ya Bukaci 'Yan Bindigan Da Ke Zamfara Su Yi Saranda


 Air Marshall Sadique Abubakar, babban hafsan sojojin saman Nigeria
Air Marshall Sadique Abubakar, babban hafsan sojojin saman Nigeria

Babban hafsan mayakan sama na Nigeria Air Marshal Sadique Abubakar ya ba 'yan bindigan Zamfara kashedi na karshe da su mika wuya idan kuma suka yi kunnen uwar shegu abun da zai biyo baya ba zai yi masu dadi ba.

Air Marshal Sadique Abubakar, babban hafsan dakaru sama na Nigeria ya gayawa 'yan bindigan dake ta da karin baya a zamfara cewa "su zo su ba da kansu, su ajiye makamansu, su bar wannan ta'addanci na kashe mutane haka siddan . Duk da yake motoci na da wahala shiga dazukan... mu a sama bamu da wannan damuwar. Saboda haka su daina wannan su ba da bindigoginsu...In sun ki abun da zai biyo baya bai da kyau".

Kalamun na babban hafsan sojojin saman Nigerian tamkar gargadine na na karshe ga 'yan bindigan dake jihar Zamfara da dazukan dake kewaye da jihar.

Aika aikar 'yan bindigan a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara, na daukar sabon salo a kusan kwane lokaci. Ibrahim Janyau, shugaban wata kungiyar samar da zaman lafiya a Zamfara ya ce al'amarin jihar ya kai lahaula wala kuwata. Ya ce kisan da ake yi a jihar Zamfara ba'a yinshi a Borno ko Yobe. A rana daya an kashe mutane 200 a kauyen 'Yar Galadima.

Ibrahim Janyau ya ci gaba da cewa maganar gaskiya sojojin sama ne maganin 'yan ta'addan saboda dazukan da jihar ke dasu. Yace matakin da aka yiwa lakabin "Diran Mikiya" da sojojin suka yi, ya kawo masu sauki gwargwado. Barayin sun bazu wasu wurare a jihar, amma ana samun nasarar kashesu. Ya kara da kiran gwamnati ta kara sojojin sama a jihar.

Amma wasu masana tsaro na ganin barin wutar da sojojin sama ke yi a jihar Zamfara ka iya sa gungun barayin su sulale zuwa cikin jihohin dake makwaftaka da Zamfara.

Sai dai Air Mashal Sadique Abubakar, ya ce farmakin da su keyi bai tsaya a Zamfara ba kawai. Jiragen yakinsu na zuwa Katsina, Birnin Gwari har ma da dazukan dake cikin jihar Niger, saboda haka duk abun dake faruwa a kasa suna gani kuma suna daukan mataki

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG