Ministocin Albarkatun Ruwa Daga Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Gudanar Da Taron Shekara-shekara 

Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

A jiya alhamis a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar Ministocin albarkatun ruwa daga kasashen yankin tafkin Chadi sun tantauna da kwararru akan hanyoyin farfado da harakokin yau da kullum a yankin mai fama da matsalolin tsaro.

NIAMEY, NIGER - Batun ceto tafkin Chadi daga halin kafewar da ya tsinci kansa ciki ne babban abinda kasashen kungiyar CBLT suka sa gaba a ‘yan shekarun nan don ganin al’umomin dake rayuwa a kewayen tafkin sun koma kan ayyukan da suka saba gudanarwa.

To amma yanayin tabarbarewar tsaron da aka shiga a ‘yan shekarun nan ya sa taron na birnin Yamai karkata akalarsa wajen nazarin hanyoyin warware matsalolin tsaro a matsayin wani matakin share fage.

Ministan albarkatun ruwa na jamhuriyar Nijer Alhaji Adamou Mahaman na ganin alamun cin nasarar shirin da aka sa gaba a bisa la’akari da yadda kowacce daga cikin kasashen yankin ta dauki wannan magana ta ceto tafkin Chadi da mahimmanci.

Tuni dai kungiyar ta fara tuntubar masu hannu da shuni domin samun hadin kansu a wannan tafiya dake bukatar makudan kudade da isashen lokaci.

An dai bayyana cewa za a damka takardun shawarwarin da taron na hadin guiwar ministoci da kwararru ya tsayar a hannun shugabannin kasashen kungiyar CLBT ta kasashen yankin tafkin Chadi don zartarwa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ministocin Albarkatun Ruwa Daga Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Gudanar Da Taron Shekara-shekara