Bayan ziyarar tsohon sakataren harkokin wajen Burtiniya a watan Agustan shekarar 2023, da kuma tattaunawar tsaro tsakanin Najeriya da Burtaniya a makon jiya, ziyarar minista Badenoch za ta dora akan kokarin da kasashen biyu ke yi na bunkasa huldar kasuwanci da kuma bude sabbin hanyoyin zuba jari.
A cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya ta fitar, a yayin da take kasar, Minista Kemi Badenoch da jakadiyar Firai Minista ta musamman a fannin kasuwanci a Najeriya, Helen Grant, za su gana da gwamnatin tarayyar Najeriya, gwamnonin jihohi, da kuma shugabannin 'yan kasuwa da masu zuba jari na Burtaniya da Najeriya.
Ta hanyar wadannan tarurrukan, ministar za ta duba halin da ake ciki da kuma damar zuba jari da harkokin kasuwanci daga ayyukan ilimi zuwa ga ayyukan more rayuwa da makamashi, da nufin samar da dubban ayyuka.
Da ya ke tsokaci kan ziyarar Badenoch Najeriya, shugaban ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Dokta Richard Montgomery ya ce, “Najeriya na daya daga cikin manyan kasashe abokan huldar Burtaniya a Afirka. Burtaniya ta himmatu wajen taimaka wa Najeriya samun damar saka hannun jari, duk da nufin samar da ayyukan yi a ƙasashenmu biyu."