Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Na Son Wuce Amurka a Zuba Hannun Jari a Afirka


Theresa May da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
Theresa May da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.

Fira Ministar Burtaniya Theresa May ta zama farin wata sha-kallo yayin ziyararta a Afirka a makon jiyo.

To amma raye-rayen kyautata cudanya da May ta yi ta yi, ba su yi rinjaye bisa babban abin da ya kai ta Afirka ba, wanda shi ne kulla dangantakar cinakayya tsakanin Afirka da Burtaniya, bayan Burtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai. May ta yi alkawarin tallafa ma kasuwannin Afirka da dala biliyan biyar ($5 bn), sannan ta yi alkawarin cewa kasarta za ta zarce Amurka har ta zama kasar da ta fi saka jari a Afirka daga cikin kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki.

Cheta Nwanze wani jami'in nazari a cibiyar bincike ta SBM ya ce Burtaniya na fadi-tashin ganin ta samu abokan cinakayya ne. "Wannan kuwa na faruwa ne saboda tsarin ficewar Burtaniya daga kungiyar EU ba ya gudana kamar yadda aka zata zai faru," in ji Nwanze.

Ita ma Shugabar Jamus Angela Merkel kwanan nan ta garzaya Afirkar, inda ta yada zango Senegal, da Najeriya da kuma Ghana, inda ita ma ta yi ta neman alfanu ga tattalin arzikin kasarta. Cikin shekaru tara a jere, kasar China ce ta kasance kasa mafi cinakayya da nahiyar Afirka, kuma da Burtaniya da Jamus su na da jan aiki, muddun burinsu shi ne cimma China.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG