Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministar Birtaniya Ta Sami Babban Koma Baya


 Farai Ministar Birtaniya Theresa May tana jawabi a majalisa
Farai Ministar Birtaniya Theresa May tana jawabi a majalisa

Har yanzu da sauran rina a kaba a kokarin Birtaniya na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai, duk da tsayar da ranar da aka yi ta ficewa daga kungiyar.

Jiya Talata Farai Ministar Birtaniya Theresa May ta fuskanci babban koma baya bayan da ‘yan Majalisu ciki har da ‘yan aware sama da 100 daga jam’iyyar ta mai mulki, suka ‘ki amicewa da daftarin yarjejeniyar May na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.

Wannan koma baya da gwamnatin ta samu zata mayarwa Birtaniya hannun agogo baya, bayan da ta tsaida ranar 29 ga watan Maris domin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

‘Yan Majalisu 202 ne kawai suka amince da daftarin, yayin da ‘yan Majalisu 432 suka kada kuri’ar kin amicewa. Wannan koma baya da aka samu ana kwatanta shi da wani irinsa da aka taba samu a baya tun shekarar alif 924, lokacin da Farai Minista Ramsay MacDonald ya sha kaye a kuri’ar da aka kada da 166, lamarin da ya haddasa rugujewar gwamnatinsa da kuma babban zaben da ya sha kaye.

Bayan da aka kada kuri’ar May ta yi kukan cewa zaben bai nuna musu komai ba, akan abububwan da zasu amince akan ficewar Burtaniya da tarayyar Turai.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG