Minista Labaru Maku Kan Fada da Gwamnan Jihar Rivers

Labaran Maku

Ministan watsa labaran NIgeria yace fadan gwamnatin tarayya da gwamnan Rivers yana kan ka’ida.
Ministan watsa labaran Nigeria Labaran Maku ya zargi ‘yanjaridu da jam’iyyun adawa akan cewa sune suke bada wata ma’ana ga cece-kuccen dake yawan barkewa tsakanin gwamnatin jihar Rivers da Gwamnatin Tarayya.

A hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa a Abuja, minista Maku yace wadanan kafofin na watsa labarai suna daukar cewa duk rigimar da ta barke a tsakanin gwamnatocin biyu siyasa ce kawai tsagaronta.

Mr. Maku yace “Doka ta hana wani ya karya dokar kasarnan. Duk kowaye ya karya doka, ya san cewa doka zai neme shi, zai hukunta shi. Kada kuma ‘yan siyasa kamar ni, su mayar da komai a kasarnan kamar siyasa.”

Dangane da jihar Rivers, Minista Maku yace “Ba maganar siyasa, sai dai kawai abunda muke gani shine ‘yan jarida, kullum suna nuna kamar aahh, ai gwamnatin Rivers, suna da gaskiya”.

Amma, a cewarsa, gwamnatin tarayya na kokarin tabattarda cewa kowa na bin doka ne.
Sai dai kuma wasu kungiyoyin kare hakkin Bil Adama na Nigeria sunce basu yarda da hakan ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Labaru Maku kan Fada da Gwamnan Jihar Rivers - 3:25