Ministan Kudi Ya Musanta Bacewar Wasu Kudade

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ministar kudin Najeriya

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ministar kudin Najeriya

A taron da gwamnonin kasar suka yi a Sokoto shugaban kungiyar gwamnonin gwamnan jihar Rivers ya ce kimanin kudi nera miliyan dubu biyar suka yi layin zana a baitunmalin gwamnatin tarayya
Gwamnan jihar Rivers wanda ke shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya shi ya yi zargin cewa kimanin kudi nera miliyan dubu biyar suka sulale daga baitunmalin gwamnatin tarayya.

Gwamna Ameichi na jihar Rivers ya ce kudaden sun bata ne daga asusun rarar albarkatun man fetur abun da ya haddasa gunaguni tsakanin gwamnonin da suka halarci taron a Sokoto. Gwamnonin sun ce bacewar kudaden ya haifar da tsaiko a harkokin ayyukan johohinsu. Gwamnan jihar Edo Oshiomole ya ce jiharsa nada haki cikin kudaden lamarin da ya sa bai iya wasu ayyuka ba. Wasu jihohin ma sun ce bacewar kudaden ya sa basu iya biyan albashi ba a watan jiya.

Gwamnan jihar Legas ya ce sun dakatar da ayyuka da dama domin rashin samun kason jihar daga gwamnatin tarayya sanadiyar bacewar kudaden. Ya ce akwai ayyuka da dama da suka yi amma sun kasa biya domin wannan matsalar. Gwamnan ya ce haba yaya za'a ce kudade har miliyan dubu biyar sun bace tamkar allura.

Amma shugaban bunkasa tattalin arziki da raya masana'antu na jihar Legas Modi Yusuf ya ce ba abun mamaki ba ne. Ya bada hujja inda ya ce wannan abun ya saba faruwa. Shugabannin kasar kuma sun sani amma sun kasa yin wani abu domin dakile irin wannan satar. Don haka idan ba wani abu aka yi cikin gaggawa ba haka za'a cigaba da tafiya.

Da aka tambayi Dr Yarima Ingama ministan kudi game da gaskiyar maganar sai ya ce wannan zukita mallaki ne, wato babu kashin gaskiya cikin maganar. Ya ce wanda ya yi maganar allawadaransa. Ya ce da akwai nera miliyan dubu tara cikin asusun kafin su yi anfani da miliyan dubu biyar. Ya ce idan haka ne sai gwamnan Rivers ya mayar da kudaden da aka ba jiharsa. Ya ce maganarsa ta fi karfin siyasa, ta zama hauka.

Idan ba'a manta ba kwamishanonin kudi sun taba yin bori domin gibin da aka samu na kason jihohi. Daga wannan asusun kudin rarar man fetur aka cika ma jihohi gibin domin su samu su cigaba da ayyukansu.

Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Kudi Ya Musanta Bacewar Wasu Kudade - 3:16