Ministan yace ya zo kasar Nijar da batutuwa guda hudu.
Yace 'yan Boko Haram manya manyan 'yan ta'ada ne. Ya kira Najeriya ta sa kaimi domin ta yakesu. Yakin da kasashen Chadi, Kamaru da Nijar keyi da 'yan Boko Haram abu ne na a jinjina masu. Yace kasar Faransa na kan gaba domin jinjinawa kasar Nijar domin irin fafitikar da ta keyi wajen kakkabe 'yan Boko Haram.
Ministan Mr. Fabius yace tarayyar Turai na kan gaba kuma da burin saka hannu domin a yaki 'yan Boko Haram.
Dangane da ziyarar ministan daga Faransa wasu 'yan kasar ta Nijar sun bayyana ra'ayoyinsu. Sun ce suna goyon bayan ziyarar iadan kuma abun da ya zo dashi na alheri ne Alla ya tabbatar. Dama mai kaunar mutum shi ne yake jajintawa idan abun bakin ciki ya faru ko kuma taya murna idan abun farin ciki ne.
Ga rahoton Shuaibu Manni
Your browser doesn’t support HTML5